Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:59:16
  • More information

Informações:

Synopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodes

  • Ra'ayoyin masu saurare kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika

    27/08/2025 Duration: 09min

    Hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta. Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la’akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta. Shin ko meye ra’ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka? Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

  • Ra'ayoyin masu sauraren kan yadda ɗimbin mutane suka rasa ayyukansu a Nijar

    25/08/2025 Duration: 11min

    A jamhuriyar Nijar, dubban mutane ne suka rasa ayyukansu yayin da ɗimbin ƴan gudun hijira suka daina samun tallafi, bayan da mahukunta suka kori mafi yawan ƙungiyoyin agaji daga gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar. Bayan korar waɗannan ƙungiyoyi da ke taimaka wa ƴan gudun hijira, a mafi yawan yankuna har yanzu gwamnatin ta gaza samar da tsarin da zai maye gurbin waɗannan ƙungiyoyi don agaza wa jama’a. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa da dama

    22/08/2025 Duration: 06min

    Yau Juma'a rana ce da mukan baiwa masu saurarenmu damar tofa albarkacin bakinsu a cikin shirinmu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikaken shirin tare da Nasiru Sani

  • Ra'ayoyin masu saurare kan alfanun sulhu da 'yanbindiga ko akasanin haka a Najeriya

    21/08/2025 Duration: 10min

    A Najeriya muhawara ta ɓarke game da buƙatar sulhu da ƴan ta’adda maimakon amfani da ƙarfin Soji, kodayake an samu mabanbantan ra’ayoyi daga ɓangaren masana a fannin na tsaro lura da yadda suka ce irin wannan sulhu ya gaza amfanarwa a yankuna da dama duk da cewa anga alfanunsa a wasu yankunan. Yaya kuke kallon wannan batu? Shin kuna ganin sulhu ko kuwa amfani da ƙarfin soji shi ne mafi  a’ala wajen yaƙi matsalolin tsaron Najeriyar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkaci bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza....

  • Ra'ayoyin masu saurare kan shirin rungumar GMO a Najeriya

    19/08/2025 Duration: 10min

    Lura da yadda jama’a ke ɗari-ɗari a game da kayan abincin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta da ake kira GMO, wannan ya sa mahukunta a Najeriya ke neman yin amfani da malaman addini domin gamsar da jama’a su rungumi irin wannan abinci. Abin neman sani a nan shi ne, shin ko kun fahinci abin da ake kira GMO? Ko a shirye ku ke domin karɓar nau’in abincin da aka canza wa ƙwayoyin halitta? Anya yin amfani da malaman addini zai sa jama’a su amince da shi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan kama jagororin ƙungiyar Ansaru a Najeriya

    18/08/2025 Duration: 10min

    Mai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Sha’anin Tsaro Nura Ribaɗo ya tabbatar da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake kira Ƴan Mahmuda su biyu, waɗanda suka jima suna addabar yankunan ƙasar. Ana dai bayyana wannan ƙungiya a matsayin babbar barazana ga matsalar tsaron ƙasar, saboda alaƙarta kai-tsaye da Alqa’ida. Shin ko wane sauyi wannan kame zai samar ta fannin tsaro a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    15/08/2025 Duration: 09min

    Yau take ranar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa da suke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, zamantewa da sauran abubuwan daban daban na rayuwa. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan yajin aikin lauyoyi a Nijar

    14/08/2025 Duration: 09min

    Lauyoyi a Jamhuriyar Nijar sun tsunduma yajin aikin kwanaki biyu daga yau Alhamis, domin nuna rashin amincewa da rusa ƙungiyoyin alƙalai da sauran ma’aikatan shari’a da gwamnatin ƙasar ta yi. Kafin rusa waɗannan ƙungiyoyi, tuni aka rusa ƙungiyoyin jami’an kare gandun daji da na kwastam da kuma illahirin jam’iyyun siyasar ƙasar. Shin, ko me za ku ce a game da wannan mataki na gwamnatin Nijar ta ɗauka? A irin wannan yanayi, ko meye makomar ƴancin gudanar da ƙungiyoyi a ƙasar? Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda Bankin Duniya ya rantawa Najeriya dala miliyan 300

    13/08/2025 Duration: 10min

    Bankin Duniya ya amince ya ranta wa Najeriya dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 460 don tallafa wa mutanen da suka ƙaurace wa matsugunansu saboda matsaloli a sassa daban daban na Arewacin ƙasar. Yanzu haka akwai mutane sama da milyan 3 da rabi da ke rayuwa a wannan yanayi, kuma mafi yawansu sun dogara da tallafi ne domin rayuwa. Shin ko waɗanne matakai suka kamata a ɗauka don tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da suka dace? Sai ku bayyana ra’ayoyinku a lambarmu ta Whatsapp da kuma shafinmu na Facebook.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan yadda ake samun ambaliyar ruwa a irin wannan lokaci

    12/08/2025 Duration: 10min

    Kusan a kowacce shekara, dai-dai wannan lokaci ne ake samun faruwar ambaliya sakamakon saukar ruwan sama mai yawa da ke haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu tarin yawa. A daidai wannan lokaci, ko wane hali ake ciki a yankunanku dangane da batun ambaliya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Nijar na ƙwace kamfanonin haƙar zinare

    11/08/2025 Duration: 10min

    Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace ilahirin kamfanonin haƙo zinare tare da shelanta cewa sun zama mallakin ƙasar, yayin da a ɗaya ɓangare ta hana fitar da duk wani nau’in dutse mai ƙima zuwa ƙetare sai tare da izinin hukuma. Hakan na zuwa ne watanni bayan ta ƙwace kamfanonin haƙo uranium matsayin mallakin ƙasar. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Waɗanne abubuwa ne suka fi ci muku tuwa a ƙwarya

    08/08/2025 Duration: 10min

    Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana kamar yadda aka saba ya baku damar fadɗn albakacin bakinku kan abubuwan da suka fi ci muku tuwo a ƙwarya a fannin lafiya, jagoranci, siyasa da kuma zamantakewa. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani

  • Ra'ayoyin masu saurare kan kalaman Falana game da matakan tattalin arziƙin Tinubu

    07/08/2025 Duration: 10min

    Bisa ga al’ada, ana cewa al’umma ta kasu ne zuwa rukuni uku, wato attajirai, da matsakaita sai kuma matalauta. To sai dai a cewar shahrarren lauya kuma mai fafutuka Femi Falana, a Najeriya mutane na rayuwa ne a ɗaya daga cikin rukuni biyu kawai: wato gungun attajirai ko kuma na talakawa, wannan kuwa sakamakon ɓullo da sabuwar siyasar tattalin arziki maras alfanu a ƙasar.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan zanga-zangar neman korar 'yan Najeriya daga Ghana

    31/07/2025 Duration: 09min

    A ƴan kwanakin nan an samu ɓarkewar zanga-zangar a Ghana, inda ƴan ƙasar ke zargin ƴan Najeriya da ke can da aikata laifuka kisan gilla da karuwanci, lamarin da ya sa masu zanga-zangar neman a koresu daga ƙasarsu. Haka nan masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa ƴan kasuwan Najeriya  sun mamaye musu kasuwanni tare da karya dokokin kasuwanci a ƙasar. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan karrama 'yan wasan Super Falcons da Tinubu yayi

    29/07/2025 Duration: 10min

    Tarihi dai ya maimaita kansa, inda tawagar Super Falcons ta Najeriya ta lashe gasar WAFCON karo na 10, bajintar da ba tawagar da ta taɓa yi. Sakamakon haka ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama ƴan wasan da lambar girmamawa ta ƙasa OON, da dala dubu dari-dari ($100,000) kowacce, da kuma gidaje a Abuja. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan bikin cika shekaru biyu da juyin mulkin Nijar

    28/07/2025 Duration: 10min

    A ranar Asabar da ta gabata, 26 ga watan Yuli Jamhuriyar Nijar ta yi bikin cika shekaru biyu a kasancewa a ƙarƙashin mulkin soji, wadanda suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum kuma suke cigaba da tsare  shi ba tare da gurfanar da shi ba. A waje daya kuma a karon farko a jawabin da ya  gabatar jagoran gwamnatin sojin Janar Abdourahmane Tchiani ya ce ya san halin ƙunci da jama’a ke ciki. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

  • Yau take ranar jin ra'ayoyin ku masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    25/07/2025 Duration: 09min

    A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan rahoton NBS na ƙaruwar tattalin arziƙin Najeriya

    23/07/2025 Duration: 09min

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ƙarin tagomashi da kashi 3 da ɗigo 13 a rubu’in farko na wannan shekarar ta 2025, saɓanin kashi 2 da ɗigo 27 yake a daidai wannan lokaci a shekarar 2024.   Wannan na zuwa ne yayin da talauci ke ci gaba da ta’azzara a tsakanin al’ummar ƙasar, kuma manoma sun gaza yin noma yadda ya kamata saboda matsalar ta’addanci. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan zanga-zangar 'yansanda a Najeriya

    22/07/2025 Duration: 09min

    A babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ɗaruruwan ƴansanda da suka yi ritaya kuma bisa ga dukkan alamu da yawun waɗanda suke bakin aiki a yanzu ne suka gudanar da zanga-zangar neman a cire su daga tsarin fanshon adashen gata, wanda suka ce babu abin da ya yi face jefa su cikin baƙin talauci bayan shafe shekaru suna wa ƙasar hidima. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....

  • Yadda Isra'ila ke kashe Falasɗinawa masu jiran tallafin abinci

    21/07/2025 Duration: 09min

    Shirin ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda Isra'ila ta mayar da guraren rabon abincin tallafi a Gaza tarkon mutuwa. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu.

page 1 from 2