Synopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodes
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rahoton NBS na ƙaruwar tattalin arziƙin Najeriya
23/07/2025 Duration: 09minHukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ƙarin tagomashi da kashi 3 da ɗigo 13 a rubu’in farko na wannan shekarar ta 2025, saɓanin kashi 2 da ɗigo 27 yake a daidai wannan lokaci a shekarar 2024. Wannan na zuwa ne yayin da talauci ke ci gaba da ta’azzara a tsakanin al’ummar ƙasar, kuma manoma sun gaza yin noma yadda ya kamata saboda matsalar ta’addanci. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan zanga-zangar 'yansanda a Najeriya
22/07/2025 Duration: 09minA babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ɗaruruwan ƴansanda da suka yi ritaya kuma bisa ga dukkan alamu da yawun waɗanda suke bakin aiki a yanzu ne suka gudanar da zanga-zangar neman a cire su daga tsarin fanshon adashen gata, wanda suka ce babu abin da ya yi face jefa su cikin baƙin talauci bayan shafe shekaru suna wa ƙasar hidima. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....
-
Yadda Isra'ila ke kashe Falasɗinawa masu jiran tallafin abinci
21/07/2025 Duration: 09minShirin ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda Isra'ila ta mayar da guraren rabon abincin tallafi a Gaza tarkon mutuwa. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rashin yiwa yara rigakafin cutuka a Najeriya a 2024
16/07/2025 Duration: 09minWani sabon rahoton Asusun kula da ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙananan yara sama da miliyan 14 ne a fadin duniya ba su samu alluran rigakafin cutukkan da ke addabar yara a shekarar 2024 ba, kuma sama da miliyan biyu daga cikin wannan adadi a Najeriya suke. Rashin wannan rigakafi na iya jefa waɗannan yara cikin hatsarin kamuwa da cutukan da ake iya samun kariya daga gare su. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...