Al'adun Gargajiya

Yadda al'adar bikin cika ciki ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa

Informações:

Synopsis

Shirin na wannan mako ya yi duba ne kan al'adar nan da ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa, wato Sallar cika ciki da ake gudanarwa bayan Sallar layya. Tsawon shekaru da wannan al’adar ta dore,ake kuma ci gaba da gudanar da ita a wurare da dama. Al'ummar Hausa da dama a birane da karkara a duk ranakun tara da goma ga watan farko na shekarar musulunci  wato Muharram, sukan gudanar da azumin da kuma raya al'adar nan mai suna cika ciki wato dai sai kaci ka koshi kuma abinci mai dadi, wasu kan amfani da iya abinda suke da shi, yayinda wasu suke karawa da hidindimu. Wani abin lura shine, yadda a yankunan karkara, idan wannan lokaci ya ƙarato, jama’a musaman mata na dukufa ne ɓangaren girki, inda a wajen gida yara matasa kan ɗora sanwa wasu lokutan su kan yi amfani da haka wajen raya al’adar nan da aka sani da  aci a cika ciki sannnan ga nishaɗi.  Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.