Bakonmu A Yau

An ɗauki hanyar samun zaman lafiya a Jamhuriyar dimokaraɗiyar Congo

Informações:

Synopsis

An fara samun haske a game da kawo ƙarshen rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda a ranar Asabar makon da ya gabata a birnin Doha na Qatar ƙasar, da kungiyar yan tawayen M23 suka rattaba hannu akan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da zumar kawo ƙarshen yakin da suke yi a tsakaninsu. A cikin yarjejeniyar, dukkannin bangarorin sun amince su tsagaita kai wa juna hare-hare tare da dakatar da farfagandar nuna ƙiyayya. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dokta Abbati Bako, masanin dangantakar ƙasa da ƙasa daga jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.