Synopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodes
-
Yadda zaɓen shugabannin Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirka ya gudana
17/03/2025 Duration: 09minA makon da ya gabata ne dai Hukumar Ƙwallonn Kafar Afirka CAF ta gudanar da zaɓenta, inda aka sake zabar Patrick Motsepe a matsayin shugaba a karo na biyu. Bayan haka ne aka gudanar da zaɓen wakilan nahiyar a Hukumar Ƙwalllon Ƙafa ta Duniya, FIFA, inda Afirka ke da wakilai 6, har da shugaban CAF mai kujerar kai-tsaye..
-
Matsalar wariyar launin fata da wasu 'yan wasa ke fuskanta
10/03/2025 Duration: 09minShirin a wannan makon zai yi duba ne kan matsalar nan ta nuna wariyar launin fata da wasu ƴan wasa ke fuskanta. Nuna wariyar launin fata a wasannin motsa jiki musamman ma kwallon ƙafa na ɗaya daga cikin ƙalubalen da ƴan wasa baƙaƙe ke fuskanta, matsala da ta shafe shekaru aru-aru ana fama da ita.Wani lokaci ƴan wasa baƙar fata dai na fuskantar cin zarafin daga magoya baya ko masu horaswa, ta hanyar zagi kai tsaye ko wata alama ta nuna kaskanci ko kuma cin fuska, duk da cewa hukumomi na ɗaukar kwararar matakai don magance matsalar.
-
Najeriya ta samu alƙalan 30 da za su busa wasannin ƙasa da ƙasa
03/03/2025 Duration: 09minShirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh, a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Hukumar Kula da Kwallon Ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa alkalan wasa 30, waɗanda hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ke bai wa bajo, don jagorantar manyan wasanni a duniya. A baya, Najeriyar na da irin waɗannan alkalai 27 ne, sai dai a bana an samu ƙarin guda uku, lamarin da ya sanya adadinsu ya kai 30, wannan adadi kuwa ya ƙunshi 22 maza sai kuma mata guda 8.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Abin da ya kamata ku sani kan wasannin zagayen ƴan 16 na gasar zakarun Turai
24/02/2025 Duration: 09minA makon da ya gabata ne Hukumar Kula da Kwallon Ƙafar Turai UEFA, ta fitar da jadawabin yadda wasannin zagayen ƴan 16, na gasar zakarun Turai zai gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........