Al'adun Gargajiya

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 4:00:18
  • More information

Informações:

Synopsis

Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Episodes

  • Ƴan China da ke Najeriya sun gudanar da bikin sabuwar shekararsu

    28/01/2025 Duration: 09min

    Shirin Al’adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar  a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta  jama’a baki daga ciki da waje. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........

  • Yadda al'adar shaɗi ko kuma Charo ke gudana tsakanin al'ummar fulani a baya

    21/01/2025 Duration: 09min

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ke kan al'adar shaɗi ko kuma Charo na sahun manyan al'adun ƙabilar fulani a ƙasashen Afrika ta yadda har sai wanda ya iya karɓaɓɓen shaɗi ke iya samun matar aure, yayinda a wasu lokutan ake gudanar da wannan al'adu a shagulgula don nishaɗi kuma jajirtacce shi ne jarumi.

  • Yadda Hausawa ke ƙoƙarin yin watsi da al'adar amfani da kwarya

    17/12/2024 Duration: 09min

    Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

  • UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na al’adun duniya

    10/12/2024 Duration: 10min

    Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al’adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al’adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa.  Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

page 2 from 2