Kasuwanci

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:46:13
  • More information

Informações:

Synopsis

Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.

Episodes

  • Gobarar kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ya tagayyara ƴan kasuwa a Ghana

    14/01/2025 Duration: 10min

    Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan asarar da ƴan kasuwar Kantamanto na ƙasar Ghana suka tafka sakamakon gobarar da ta lakume kasuwar ƙurmus.Hukumomi a Ghana sun ce mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ranar 2 ga watan Janairun wannan shekara ta 2025 ta lakume sama da shaguna dubu 7 tare da tagayyara ƴan kasuwa sama da dubu 30, inda akalla mutun guda ya mutu wasu 14 suka jikkata.

  • Yadda aka samu hauhawan farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

    18/12/2024 Duration: 10min

    Shirin kasuwa akai miki dole zai mayar da hankali ne kan yadda farashin kayan abinci ya ke hauhawa a Najeriya, daidai lokacin da  ake shirye shiryen bukukuwan Kirsimeti, musamman a kudancin ƙasar, inda a halin yanzu farashin buhun albasa yakai sama da ₦320,000 yayin da buhun shinkafa ƴar gida yakai ₦120,000. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........

page 2 from 2